لِثَلَاثِ رَكَعَاتٍ مِنْ اللَّيْلِ إلَى رَكْعَةٍ قَضَتْ الصَّلَاةَ الْأُولَى فَقَطْ
Idan kuma Haila ta zo mata saura raka’a hudu (4) yini ya kare ko kasa ga haka, har zuwa raka’a daya (1), ko kuma raka’oi uku (3) ya rage dare ya kare zuwa rak’a daya (1), to ita sallar farko kawai za ta ranka (Azahar da rana, Magriba da dare)
وَاخْتُلِفَ فِي حَيْضِهَا لِأَرْبَعِ رَكَعَاتٍ مِنْ اللَّيْلِ فَقِيلَ مِثْلُ ذَلِكَ، وَقِيلَ إنَّهَا حَاضَتْ فِي وَقْتِهِمَا فَلَا تَقْضِيهِمَا
Amma an yi sabani a cikin hailarta idan ya rage saura raka’a hudu (4) dare ya kare, wasu Malamai sun fadi irin haka (Za ta ranka Sallar kamar yadda aka ambata a baya). Wasu kuma sun ce lallai ta yi hailarta ne a cikin lokcinta (Lokacin sallolin), ba za ta ranka sallolin ba.
الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتُ وَالصَّلَاةُ وَالسَّلَامُ عَلَى المبعوث رحمة للعالمين نبينا محمدصلى الله عليه وسلم
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda da ni’imarSa ne ayukka na kwarai suke kammala, tsira da Aminci su tabbata a kan wanda aka aiko shi domin Rahma ga Talikai, wato Annabinmu Muhammadu Sallahu alaihi wa sallam.
Shiga nan Domin Samun Shauran Darussan...
Share this with family and friends to spread awareness
0 Comments