Farilla. Idan a cikin Sallar Farilla ne, to zai yi Sujadar kabliyya ko Kuma Sujadar Ba’adiyya a bagirensu.
المسئلة الخامسة
ومن قام إلى ثالثة في النافلة فإن تذكر قبل عقد الركوع رجع وسجد بعد السلام
Mas’ala ta Biyar
Wanda ya mike tsaye domin kawo Raka’a ta uku (3) a cikin Sallar Nafila, to idan ya tuna kafin ya yi Ruku’i, ya dawo, sai ya yi Sujada Ba’adiyya.
وإن عقد الثالثة تمادى وزاد الرابعة وسجد قبل السلام. لأنه نقص جلوس الأول بخلاف الفريضة, فإنه يرجع متى ما ذكر ويسجد بعد السلام. لأنه لا يزاد على الفريضة بعد تمامها إن علم
Idan kuma ya riga ya kulla Raka’a ta uku (3), to ya cigaba da Sallarsa sai ya kara ta hudu (4), sai ya yi Sujada Kabliyya, domin shi ya rage zama na farko. Wannan ya saba ma Sallar Farilla, domin shi zai dawo a lokacin da ya tuna, sai yayi Sujada Ba’adiyya. Domin ba a yin kari a kan Farilla bayan cikar ta, idan ana sane.
0 Comments