الركعة ويزيد أخرى ويتمادى ويكون سجوده كما ذكرنا في تارك السجود، يعني يسجد بعد السلام بعد إصلاحه
Mas’ala ta Farko
Wanda ya manta da karatun Fatiha a cikin Sallar Nafila, sai ya tuna bayan ya yi Ruku’i, to ya cigaba da Sallarsa, sai ya yi sujada kabliyya. Wannan ya saba ma Sallar Farilla. Idan cikin Sallar farilla ne, to zai yar da wannan Raka’ar, sai ya kara wata Raka’a. Kuma Sujadar Rafkanuwarsa za ta kasance kamar yadda muka ambata game barin sujada. Abinda ake Nufi shi ne zai zai yi sujada Ba’adiyya.
المسئلة الثانية والثالثة والرابعة
ومن نسى السورة أو الجهر أو السر في النافلة وتذكر بعد الركوع تمادى ولا سجود عليه بخلاف الفريضة فإنه يسجد قبلية أو بعدية في محلهما.
Mas’ala ta Biyu, ta Uku, da ta Hudu
Wanda ya manta da karatun sura ko Bayyanawa ko Asirtawa a cikin Sallar Nafila, sai ya tuna bayan ya yi Ruku’i, to ya cigaba da Sallarsa, babu Sujadar Rafkanuwa a gare shi. Wannan ya saba ma Sallar
0 Comments