Ticker

6/recent/ticker-posts

Fadakarwa Game da Hade Sallar Magriba da Isha’i Saboda Ruwan Sama (2)


kadan a zancen Maliku, sa’annan a tayar da ita a cikin Masallaci sai a sallace ta.

ثُمَّ يُؤَذِّنُ لِلْعِشَاءِ فِي دَاخِلِ الْمَسْجِدِ وَيُقِيمُ ثُمَّ يُصَلِّيهَا ثُمَّ يَنْصَرِفُونَ وَعَلَيْهِمْ إسْفَارٌ قَبْلَ مَغِيبِ الشَّفَقِ

Sa’annan a yi Kiran Sallar Isha’i a cikin Masallaci Kuma a ta yarda ita sa’annan a Sallace ta, sai mutane su tafi kuma a gare su akwai sauran haske kafin boyewar Shafaki.

ويكره التنفل بينهما، وجاز للمنفرد بالمغرب يجدهم  بالعشاء أن يصلي معهم، والمعتكف بمسجد، وجاز أيضا لمجاورهم وغريب تباعهم، وجاز  أيضا أن يصليهما جمعا إن انقطع بعد الشروع

Kuma an karhanta yin Sallar Nafila a tsakaninsu (Idan an hada Magriba da Isha’i) Kuma yana halasta ga wanda ya yi  Sallar Magriba shi kadai, sai ya same su suna Sallar Isha’i, da ya yi Sallar Isha’i tare da su. Haka nan shi ma wanda yake I’itikafi a cikin Masallacin. Haka nan yana halasta ga wanda yake makwabtakada su da Kuma bako ya halasta ya bi su. Kuma yana halasta su sallace su (Magriba da Isha’i) a hade idan dalilin hadewar ya yanke bayan an fara.


 

Shiga nan Domin Samun Shauran Darussan...

Share this with family and friends to spread awareness

Post a Comment

0 Comments