Ticker

6/recent/ticker-posts

Fadakarwa Game da Hade Sallar Magriba da Isha’i Saboda Ruwan Sama


wadanda suke sanya matsakaitan Mutane rufe kai. Kuma duk daya ne ya kasance (Ruwan) suna aukuwa ne ko kuma zasu auku, kuma ana iya sanin hakan ne ta hanyar kusanci (wato alamu). Haka nan misalin ruwan kankara, ko masu sanyi wadanda suka saba ma al’ada.

وكذلك في طين وظلمة، وأما الطين وحدها لا يجمع لها  على المشهور، وأما الظلمة وحدها فالتفاق أهل المذهب على أنه لا يجمع لها وحدها

Haka nan kuma an yi rangwame game da hada  Magriba da Isha’i a saboda  tabo da kuma duhu (Wato duhun karshen wata). Amma tabo shi  kadai,  ba za a  hada Magriba da Isha’i  saboda shi ba, a kan zance mafi inganci. Amma shi duhu  shi kadai,  a ittifakin  ma’abota wannan  mazhaba, ba za a hada Magriba  da  Isha’i ba a kan  shi, shi kadai ba.

وصفته: أن يؤذن للمغرب أول الوقت خارج المسجد ثم يؤخر قليلا في قول مالك، ثم يقيم في داخل المسجد ويصليها

Kuma siffar yadda ake yin Jam’in (Magriba da Isha’i) shi ne za a yi kiran Sallar Magriba a farkon lokacinta a wajen Masallaci, sa’annan a jinkirta tayar da ita


Post a Comment

0 Comments