The Excellence of Observing Fasting on the Day of 'Ashura' and Tasu'a (i.e., 9th & 10th of Muharram)
Falalar Yin Azumi Ranar Ashura da Tasu'a (wato 9 da 10 ga Muharram)
وعن ابن عباس رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم صام يوم عاشوراء، وأمر بصيامه. ((متفق عليه))
Ibn 'Abbas (May Allah be pleased with them) reported: The Messenger of Allah (ﷺ) observed Saum (fasting) on the day of 'Ashura' and commanded us to fast on this day. [Al-Bukhari and Muslim].
An karbo daga Ibn Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya azumci azumi a ranar Ashura, kuma ya umarce mu da mu azumci wannan rana. [Bukhari da Muslim].
Riyad as-Salihin 1251
حَدَّثَنَا عُبَيْدُ اللَّهِ بْنُ مُوسَى، عَنِ ابْنِ عُيَيْنَةَ، عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي يَزِيدَ، عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ ـ رضى الله عنهما ـ قَالَ مَا رَأَيْتُ النَّبِيَّ صلى الله عليه وسلم يَتَحَرَّى صِيَامَ يَوْمٍ فَضَّلَهُ عَلَى غَيْرِهِ، إِلاَّ هَذَا الْيَوْمَ يَوْمَ عَاشُورَاءَ وَهَذَا الشَّهْرَ. يَعْنِي شَهْرَ رَمَضَانَ.
Narrated Ibn `Abbas: I never saw the Prophet (ﷺ) seeking to fast on a day that he favored more than another except this day, the day of 'Ashura', and this month, meaning the month of Ramadan.
An karbo daga Ibn Abbas ya ce: “Ban taba ganin Annabi (SAW) yana neman azumtar ranar da ya fi falala fiye da wani ba face wannan ranar, wato ranar Ashura, da wannan wata, ma’ana watan Ramadan.
Sahih al-Bukhari 2006
عَنْ أَبِي قَتَادَةَ اَلْأَنْصَارِيِّ - رضى الله عنه - { أَنَّ رَسُولَ اَللَّهِ - صلى الله عليه وسلم -سُئِلَ عَنْ صَوْمِ يَوْمِ عَرَفَةَ. قَالَ: " يُكَفِّرُ اَلسَّنَةَ اَلْمَاضِيَةَ وَالْبَاقِيَةَ ", وَسُئِلَ عَنْ صِيَامِ يَوْمِ عَاشُورَاءَ. قَالَ: " يُكَفِّرُ اَلسَّنَةَ اَلْمَاضِيَةَ " وَسُئِلَ عَنْ صَوْمِ يَوْمِ اَلِاثْنَيْنِ, قَالَ: " ذَاكَ يَوْمٌ وُلِدْتُ فِيهِ, وَبُعِثْتُ فِيهِ, أَوْ أُنْزِلَ عَلَيَّ فِيهِ " } رَوَاهُ مُسْلِمٌ 1 .
1 - صحيح. رواه مسلم ( 1162 ) ( 197 )، وساقه الحافظ بتقديم وتأخير.
Abu Qatadah Al-Ansari (RAA) narrated, ‘The Messenger of Allah (ﷺ) was asked about fasting on the day of Arafah (the 9th of the month of Dhul Hijjah). He replied, "Fasting on the day of Arafah is an expiation for the preceding year and the following year.” He was also asked about fasting on the day of Ashura (the 10th of the month of Muharram). He replied, “Fasting on the day of Ashura is an expiation for the preceding year.” The Messenger of Allah (ﷺ) was also asked about fasting on Monday, and he replied, "This is the day on which I was born and the day on which I was sent (with the Message of Islam) and the day on which I received revelation." Related by Muslim.
An karbo daga Abu Qatadah Al-Ansari (RA) ya ce, “An tambayi Manzon Allah (SAW) game da azumin ranar Arafah (9 ga watan Dhul Hijjah). Sai ya karva masa da cewa: “Azumtar ranar Arafah kaffara ce ta shekarar da ta gabace ta da kuma shekara mai zuwa”. An kuma tambaye shi game da azumin ranar Ashura (10 ga watan Muharram). Sai ya ce: “Azumtar ranar Ashura kaffara ce ta shekarar da ta gabata. Haka kuma an tambayi Manzon Allah (SAW) game da azumin ranar Litinin, sai ya ce: “Wannan ita ce ranar da aka haife ni da ranar da aka aiko ni (da sakon Musulunci) da ranar da aka fara saukar min da wahayi”.
Bulugh al-Maram: 5/31
وَحَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ، وَابْنُ، نُمَيْرٍ قَالاَ حَدَّثَنَا أَبُو أُسَامَةَ، عَنْ أَبِي عُمَيْسٍ، عَنْ قَيْسِ بْنِ مُسْلِمٍ، عَنْ طَارِقِ بْنِ شِهَابٍ، عَنْ أَبِي مُوسَى، - رضى الله عنه - قَالَ كَانَ يَوْمُ عَاشُورَاءَ يَوْمًا تُعَظِّمُهُ الْيَهُودُ وَتَتَّخِذُهُ عِيدًا فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم " صُومُوهُ أَنْتُمْ " .
Abu Musa (Allah be pleased with him) reported: The day of 'Ashura was one which the Jews respected and they treated it as Id. The Messenger of Allah (ﷺ) said: You also observe fast on this day.
An karbo daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Ranar Ashura ita ce ranar da Yahudawa suke girmama ta, suka dauke ta a matsayin Idi. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku kuma ku yi azumin wannan rana.
Sahih Muslim 1131a
أَخْبَرَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي النَّضْرِ، قَالَ حَدَّثَنَا أَبُو إِسْحَاقَ الأَشْجَعِيُّ، - كُوفِيٌّ - عَنْ عَمْرِو بْنِ قَيْسٍ الْمُلاَئِيِّ، عَنِ الْحُرِّ بْنِ الصَّيَّاحِ، عَنْ هُنَيْدَةَ بْنِ خَالِدٍ الْخُزَاعِيِّ، عَنْ حَفْصَةَ، قَالَتْ أَرْبَعٌ لَمْ يَكُنْ يَدَعُهُنَّ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم صِيَامَ عَاشُورَاءَ وَالْعَشْرَ وَثَلاَثَةَ أَيَّامٍ مِنْ كُلِّ شَهْرٍ وَرَكْعَتَيْنِ قَبْلَ الْغَدَاةِ .
It was narrated that Hafsah said: "There are four things which the Prophet never gave up: Fasting 'Ashura', (fasting during) the ten days, (fasting) three days of each month, and praying two Rak'ahs before Al-Ghadah (Fajr)."
An karbo daga Hafsah ta ce: “Abubuwa hudu ne Annabi bai bar su ba: Azumin Ashura’ (Azumin) kwanaki goma, da yin azumin kwana uku na kowane wata, da yin sallar raka’a biyu gabanin Al-Ghadah (fajir).
Sunan an-Nasa'i 2416
وَعَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ: مَا رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتَحَرَّى صِيَامَ يَوْمٍ فَضَّلَهُ عَلَى غَيْرِهِ إِلَّا هَذَا الْيَوْمَ: يَوْمَ عَاشُورَاءَ وَهَذَا الشَّهْرُ يَعْنِي شَهْرَ رَمَضَان
Ibn ‘Abbas said, "I never saw the Prophet singling out any day’s fast and considering it more excellent than another, except this day, the day of ‘Ashura’,* and this month, meaning the month of Ramadan." *The 10th of Muharram.
(Bukhari and Muslim.)
Ibn Abbas ya ce, “Ban taba ganin Annabi ya kebe azumin wata yini ba, kuma ya fifita shi fiye da wani ba, sai wannan ranar, wato ranar Ashura’ (10 ga Muharram), da wannan wata, ma’ana watan Ramadan.
(Bukhari da Muslim)
Mishkat al-Masabih 2040
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَدِمَ الْمَدِينَةِ فَوَجَدَ الْيَهُودَ صِيَامًا يَوْمَ عَاشُورَاءَ فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا هَذَا الْيَوْمُ الَّذِي تَصُومُونَهُ؟» فَقَالُوا: هَذَا يَوْمٌ عَظِيمٌ: أَنْجَى اللَّهُ فِيهِ مُوسَى وَقَوْمَهُ وَغَرَّقَ فِرْعَوْنَ وَقَوْمَهُ فَصَامَهُ مُوسَى شُكْرًا فَنَحْنُ نَصُومُهُ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَنَحْنُ أَحَقُّ وَأَوْلَى بِمُوسَى مِنْكُمْ» فَصَامَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَمَرَ بصيامه
Ibn ‘Abbas said that God’s messenger came to Medina and found the Jews observing the fast on the day of ‘Ashura’, so he asked them what was the significance of that day which they were observing and they replied, “It is a great day on which God delivered Moses and his people and drowned Pharaoh and his people; so Moses observed it as a fast out of gratitude, and we do so also.” He said, “We have more right, and we have a closer connection with Moses than you have,” so God’s messenger observed it as a fast himself and gave orders that it should be observed.
(Bukhari and Muslim.)
Ibn Abbas ya ce: Manzon Allah (SAW) ya zo Madina ya tarar da Yahudawa suna azumin ranar Ashura, sai ya tambaye su mene ne ma'anar wannan ranar da suke kiyayewa, sai suka ce: "Rana ce mai girma wadda Allah ya kubutar da Musa da mutanensa, ya nutsar da Fir'auna da mutanensa, sai Musa ya yi azumi domin godiya, mu ma muna yin haka." Ya ce: “Mu ne mafi cancanta, kuma mun fi kusanci da Musa fiye da ku,” sai Manzon Allah (SAW) ya yi azumi da kansa, kuma ya yi umarni da a yi shi.
(Bukhari da Muslim)
Mishkat al-Masabih 2067
حَدَّثَنِي عَمْرٌو النَّاقِدُ، حَدَّثَنَا سُفْيَانُ، عَنِ الزُّهْرِيِّ، عَنْ عُرْوَةَ، عَنْ عَائِشَةَ، - رضى الله عنها - أَنَّ يَوْمَ، عَاشُورَاءَ كَانَ يُصَامُ فِي الْجَاهِلِيَّةِ فَلَمَّا جَاءَ الإِسْلاَمُ مَنْ شَاءَ صَامَهُ وَمَنْ شَاءَ تَرَكَهُ .
'A'isha (Allah be pleased with her) reported. In the pre-Islamic days fast was observed on the day of Ashura, but with the advent of Islam (its position was ascertained as that of a voluntary fast). Then he who wished to fast fasted, and he who liked to abandon it abandoned it.
An ruwaito A'isha (Allah Ya yarda da ita). A zamanin jahiliyya ana yin azumin ranar Ashura, amma da zuwan Musulunci (an tabbatar da matsayinsa a bagiren zabi). Mai son yin azumi ya yi azumi, wanda ya so ya bar shi.
Sahih Muslim 1125c
حَدَّثَنِي يَحْيَى، عَنْ مَالِكٍ، عَنْ هِشَامِ بْنِ عُرْوَةَ، عَنْ أَبِيهِ، عَنْ عَائِشَةَ، زَوْجِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم أَنَّهَا قَالَتْ كَانَ يَوْمُ عَاشُورَاءَ يَوْمًا تَصُومُهُ قُرَيْشٌ فِي الْجَاهِلِيَّةِ وَكَانَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم يَصُومُهُ فِي الْجَاهِلِيَّةِ فَلَمَّا قَدِمَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم الْمَدِينَةَ صَامَهُ وَأَمَرَ بِصِيَامِهِ فَلَمَّا فُرِضَ رَمَضَانُ كَانَ هُوَ الْفَرِيضَةَ وَتُرِكَ يَوْمُ عَاشُورَاءَ فَمَنْ شَاءَ صَامَهُ وَمَنْ شَاءَ تَرَكَهُ .
Yahya related to me from Malik from Hisham ibn Urwa from his father that A'isha, the wife of the Prophet, may Allah bless him and grant him peace, said, "The day of Ashura was a day the Quraysh used to fast in the jahiliyya, and the Messenger of Allah, may Allah bless him and grant him peace, used also to fast it during the jahiliyya. Then when the Messenger of Allah, may Allah bless him and grant him peace, came to Madina he fasted it and ordered that it be fasted. Then Ramadan was made obligatory, and that became the fard instead of Ashura, but whoever wanted to, fasted it, and whoever did not want to, did not fast it."
Yahya ya ruwaito mini daga Malik daga Hisham bn Urwa daga babansa cewa, A’isha matar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta ce: “Ranar Ashura rana ce da Kuraishawa suke azumtar jahiliyya, kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana azumtar sa a cikin jahiliyya, sannan kuma Manzon Allah (S.W.A) ya azumce shi. Sai aka wajabta Ramadan, wannan ya zama farilla maimakon Ashura, amma wanda ya so ya azumce shi, wanda kuma bai so ba, ba sai ya azumce shi ba.
Muwatta Malik: 506670
Shiga nan Domin Samun Shauran Daily Update...
Share this with family and friends to spread awareness
0 Comments