Ticker

6/recent/ticker-posts

Fadakarwa Game da Hada Salloli guda biyu ga matafiyi (2)


Idan Mutum ya yi tafiya a farkon lokacin Sallar farkon (Azahar), kuma ya sauka a zangonsa (Wato tasha ko inda zai cigaba da tafiya), ya samu a wannan lokaci ya hade Sallolin (Azahar da La’asar). Wannan shi ake kira Jam’i na hakika.


وَلِلْمَرِيضِ أَنْ يَجْمَعَ إذَا خَافَ أَنْ يُغْلَبَ عَلَى عَقْلِهِ عِنْدَ الزَّوَالِ وَعِنْدَ الْغُرُوبِ


Haka nan mara lafiya ya samu ya hade Sallolin (Azahar da La’asar) idan yana jin tsoron gushewar Hankalinsa a lokacin da rana ta karkata, haka nan (Magariba da Isha’i) Lokacin da rana ta fadi.


وَإِنْ كَانَ الْجَمْعُ أَرْفَقُ بِهِ لِبَطْنٍ بِهِ وَنَحْوِهِ جَمَعَ وَسْطَ وَقْتِ الظُّهْرِ وهو  آخر المختار وَعِنْدَ غَيْبُوبَةِ الشَّفَقِ يجمع بين  المغرب والعشاء


Idan kuma hade sallolin (Azahar da La’sar) ya kasance ya fi sauki a gare shi saboda wani ciwon ciki da yake da, ko makamacin sa, to ya hade (Azahar da La’asar) a tsakiyar lakacin Sallar Azahar, wato shi ne karsen zababben lokacin. Haka nan kuma a lokacin da shafaki ya boye, zai iya hadewa tsakanin Magriba da Isha’i. 


Shiga nan Domin Samun Shauran Darussan...

Share this with family and friends to spread awareness

Post a Comment

0 Comments