Haka nan ba a hade Salloli idan dalilin hadewar ya faru bayan an gama Sallar farko (Magriba). Hakanan mace a cikin gidanta ba za ta hade ba. haka nan shi ma mai rauni a cikin gidanshi, shi ma ba zai hadeba. Haka nan wanda yake shi kadai a cikin Masallacin sa, kamar jama’ar da babu bukatar hadewa a garesu, duk wadannan ba za su hade ba.
التنبيه: في جمع بين الصلاتين للمسافر
وللمسافر إذا جد السير فله أن يجمع بين الصلاتين في ءاخر وقت المختار الظهر وأول وقت العصر، وكذلك المغرب والعشاء، وهذا جمع صوري.
Fadakarwa Game da Hada Salloli guda biyu ga matafiyi
Shi matafiyi, idan tafiyar ta yi wahala a gare shi, ya samu ya hade Salloli guda biyu (2) (Azahar da La’asar) A karshen zababben lokacin Sallar Azahar wato farkon Lokacin Sallar La’asar. Haka nan kuma tsakanin Magriba da Isha’i. Wannan shi ne ake cewa jam’u suri.
وَإِذَا ارْتَحَلَ فِي أَوَّلِ وَقْتِ الصَّلَاةِ الْأُولَى وهو نازل بمنهل جَمَعَ حِينَئِذٍ، وهذا هو جمع الحقيقي
Shiga nan Domin Samun Shauran Darussan...
Share this with family and friends to spread awareness
0 Comments